Home Labaru Kiwon Lafiya Yawan Masu Cutar Coronavirus A Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa 22

Yawan Masu Cutar Coronavirus A Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa 22

1057
0

Wasu karin mutum 10 sun kamu da cutar COVID-19 a Najeriya.

Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC, ta ce yanzu adadin masu dauke da cutar a Najeriya ya karu zuwa 22.

NCDC ta ce sabbin masu dauke da CORONAVIRUS din sun hada da mutum uku a Abuja da wasu mutum 7 a jihar Legas.

Sanarwar da NCDC ta fitar ta ambato ma’aikatar Lafiya ta Tarayya na cewa 9 daga cikin marasa lafiyan sun dawo ne daga kasashen waje a cikin makon da ya gabata.

Mutum na 10 kuma ya kamu ne ta sanadiyyar mu’amala da wadanda suka dawo daga ƙasashen waje.

Mutanen na samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, da kuma Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa da ke Legas.