Home Labarai Yawan Ciyo Bashi: Atiku Ya Gargaɗi Tinubu

Yawan Ciyo Bashi: Atiku Ya Gargaɗi Tinubu

284
0
Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce yawaitar ciyo basuka da gwamnatin Bola Tinubu ke yi zai ƙara jefa tattalin arzikin Najeriya cikin ƙunci.

Tsohon ɗantakarar shugaban kasa ya kuma soki yadda majalisar dokoki ke amincewa da buƙatar ciyo basukan, waɗanda a cewar sa suke ƙara jefa ƙasa cikin ƙangin bashi.

Atiku ya bayyana haka ne a wani rubuta da ya wallafa a shafin sa na Facebook, inda ya ce, rahoton da bankin duniya ya fitar kwanan nan,

wanda ke nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta uku da ta fi cin bashi daga hukumomin kuɗi na duniya abin damuwa ne.

Ya ƙara da cewa Najeriya na ƙara nutsewa a cikin bashi, sannan majalisar dokoki suna taimakawa. Tinubu ya bayyana a watan Yuli cewa hukumar tattara haraji da kwastam sun tara kuɗin shiga da ba a taɓa tarawa ba.

To me ya sa ake cin bashin? akwai wani abu da suke ɓoyewa ƴan Najeriya.”

Atiku ya ƙara da cewa yawan cin bashin yana ƙara takurawa tattalin arzikin.

Leave a Reply