Home Labaru Yarjejeniyar Tsaro: Hukumomi A Mali Sun Maida Martani Da Kakkausar Murya

Yarjejeniyar Tsaro: Hukumomi A Mali Sun Maida Martani Da Kakkausar Murya

18
0

Hukumomin Mali sun mayar da martani da kakkausan lafazi kan kasashen da ke zargin su da neman kulla yarjejeniyar tsaro dan dauko sojojin hayar Wagner daga Rasha.

A cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan Lahadi, ma’aikatar harkokin wajen Malin ta ce kasar na da ‘yancinta na tattaunawa da duk wani da take ganin zai kaita ga tabbatar da tsaro da doka da oda.

Sai dai duk da yake bata fito fili ta ambaci wata kasar ba, sanarwar ta kuma kara da cewa ba wata kasar da za ta zabar wa Mali abokiyar dasawa ko hulda.

Ko a yayin wata ganawa da manela labarai a baya firaministan gwamnatin wucin gadin kasar ta Mali Choguel Kokalla Maïga, ya ce kasar na da hurumin yin abinda taga dama.

Kasashen Jamus da Faransa da ma kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS, sun yi kakkausar suka kan matakin kasar Mali na kulla yarjejeniyar tsaro da wani kamfanin sojojin haya mai suna Wagner na kasar Rasha, suna masu cewa matakin ka iyya dagula al’amurra a Mali da ma yankin yammacin Afirka.