Home Labaru Karshen Rayuwa: Tsohon Mataimakin Babban Bankin Najeriya Obadiah Mailafia Ya Mutu

Karshen Rayuwa: Tsohon Mataimakin Babban Bankin Najeriya Obadiah Mailafia Ya Mutu

14
0

Tsohon mataimakin Babban Bankin Najeriya Dr Obadiah Mailafiya, ya mutu kamar yadda uwargidan sa ta tabbatar inda ta ce ya mutu ne a asibitin Gwagwalada da safiyar Lahadi bayan gajeruwar rashin lafiya.

Obadiah Mailafia dai ɗan asalin jihar Kaduna ne kuma masanin tattalin arziki da harakokin banki.

Kafin rasuwar sa ya rike mukamin mataimakin Babban Bankin Najeriya tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007.

Marigayin ya taɓa tayar da ƙura a Najeriya, a wata hira da aka yi da shi inda ya yi zarge-zarge da dama, ciki har da zargin ɗaya daga cikin gwamonin arewacin Najeriya da jagorantar ƙungiyar Boko Haram.

Sai dai daga baya Obadiah ya ce a kasuwa ya tsinci zancen a bakin wasu Fulani.