Home Labaru ‘Yancin Addini: Nijeriya Ta Maida Wa Amurka Kakkausan Martani

‘Yancin Addini: Nijeriya Ta Maida Wa Amurka Kakkausan Martani

477
0
Lai Mohammed, Ministan Yada Labarai
Lai Mohammed, Ministan Yada Labarai

Gwamnatin tarayya, ta yi watsi da wani rahoton Amurka da ke zargin gwamnatin Nijeriya da tauye ‘yancin jama’a na yin addinin da su ka ga dama.

Ministan yada labarai Lai Mohammed, ya kwatanta ratohon da hukumar kare ‘yancin yin addini ta Amurka ke fitarwa duk shekatar a matsayin abin da aka dade da yin watsi da shi.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Segun Adeyemi ya fitar, Ministan ya ce ‘yan Nijeriya su na da cikakken ‘yancin gudanar da addinin su.

Ministan, ya zargin marasa kishi, musamman daga cikin malaman addini da ‘yan siyasa, wadanda su ka yi amfani da addini domin samun kuri’u a zaben da ya gabata.

Sanarwar, ta yi mamakin yadda rahoton da sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fitar, wanda ya yi rashin sa’ar fadawa tarkon mutanen da ke iya jefa Nijeriya cikin matsala saboda adawa ko son zuciya.

Ya ce kokarin miyagun na sanya addini a rikicin manoma da makiyaya da sauran rigingimu marasa nasaba da addini ne ya sa rahoton ke ganin gwamnati ba ta yin abin da ya dace game da ‘yancin addini a Nijeriya.