‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane bakwai a kauyen
Warkan da ke yankin Atyap a karamar hukumar Zangon Kataf
ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun kuma kona gidaje da dama tare da salwantar da tarin dukiyoyi, yayin da wadanda su ka samu raunuka ba za su misaltu ba.
Wata Majiya ta ce, maharan sun afka kauyen ne, inda su ka ci karen su babu babbaka, yayin da mahukunta ke kokarin gano yawan mutanen da su ka samu raunuka.
Wasu mazauna yankin, sun koka da yadda mahukunta ba su daukar matakai masu tsauri da za su dakile irin wadannan hare-haren da ke faruwa na tsawon lokaci musamman a yankin Atyap.














































