Home Labaru ‘Yan Sandan Zamfara Sun Ƙaryata Kama Sojoji 7 Masu Alaƙa Da ‘Yan...

‘Yan Sandan Zamfara Sun Ƙaryata Kama Sojoji 7 Masu Alaƙa Da ‘Yan Bindiga

13
0
ZAMFARA-CP-Ayuba-Elkanah

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara, ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ta kama wasu jami’an soji guda bakwai da ake zargin su na da alaƙa da ayyukan ‘yan bindiga.

Wata Sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Zamfara SP Mohammed Shehu ya raba wa manema labarai, ta ce babu wani soja da ‘yan sanda su ka kama, saɓanin yadda ake yaɗawa a kafofin sada zumunta.

Sanarwar, ta ce labarin ƙarya ne ake yaɗawa, tare da yin gargaɗi ga masu yaɗa labarun ƙarya cewa duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma.