Home Home ‘Yan Sanda Sun Kama Zaɓabben Ɗan Majalisar Wakilai Na Nnpp A Kano

‘Yan Sanda Sun Kama Zaɓabben Ɗan Majalisar Wakilai Na Nnpp A Kano

35
0
‘Yan sanda a jihar Kano, sun kama ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Dala a majalisar wakilai Sani Madakin Gini, bisa laifin mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba.

‘Yan sanda a jihar Kano, sun kama ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Dala a majalisar wakilai Sani Madakin Gini, bisa laifin mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da haka, inda ya ce yanzu haka ana bincike a kan ɗan majalisar.

Kakakin ‘yan sandan, ya ce ɗan majalisar ya na hannun su a halin yanzu kuma su na ci gaba da bincike, ya na mai cewa ‘yan sanda ba za su yi ƙasa a gwiwa ba, a ƙoƙarin ganin doka ta yi aiki a kan duk wanda da aka kama da laifi.

Kama Sani Madakin Gini da aka zaɓa a karkashin jam’iyyar NNPP dai ya haifar da damuwa da martani daga bangarori daban-daban.