Home Labarai BUDE IYAKOKI: SYRIA TA BAYAR DA DAMAR SHIGAR DA KAYAN AGAJI YANKIN...

BUDE IYAKOKI: SYRIA TA BAYAR DA DAMAR SHIGAR DA KAYAN AGAJI YANKIN DA GIRGIZAR KASA TA SHAFA

124
0
People walk past collapsed buildings following a devastating earthquake in the town of Jinderis, Aleppo province, Syria, Thursday, Feb. 9, 2023. The quake that razed thousands of buildings was one of the deadliest worldwide in more than a decade. (AP Photo/Ghaith Alsayed)

Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya ce shugaba Bashar al-Assad na Syria ya amince da bude karin iyakokin kasar 2 domin samun sukunin kai agaji ga wadanda ibtila’in girgizar kasa ya shafa akan iyakar kasar da Turkiya wadda zuwa yanzu ta kashe mutane fiye da dubu 37 a kasashen biyu.

Wannan mataki na Syria na zuwa ne kwana guda bayan ganawar shugaba Bashar al-Assad da Antonio Guterres a birnin Damascus inda suka tattauna kan yadda za a taimakawa mutanen da girgizar kasa ta tagayyara a yankunan na kan iyakar kasar da Turkiyya.

Guterres ya ce Assad ya amince ya bude iyakokin Bab Al-Salam da Al Raee daga bangaren Turkiya zuwa arewa maso yammacin Syria na tsawon watanni 3 domin a taimaka wa wadanda ke matukar bukatar agajin gaggawa.

A cewar sa adadin wadanda suka mutu sakamakon wannan girgizar kasar na ci gaba da karuwa,  kuma wadanda suka tsallake rijiya da baya daga ibtila’in na cikin mummunan yanayi na matsanacin sanyi, musammama a Syria, inda yaki ya daidaita.

Leave a Reply