Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Kone Ofishin Sanata Barau

‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Kone Ofishin Sanata Barau

72
0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu ’yan daba 13 da ake zargi da hannu wurin kone ofishin Barau Jibrin, Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa da safiyar ranar Alhamis din nan a Kano.

Bayanai sun rawaito cewar an cafke ’yan daban ne dauke da muggan makamai da miyagun kwayoyi.

Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce tuni jami’an rundunar suka shawo kan lamarin, kuma an fara gudanar da bincike kan wanda aka cafke kafin mika su kotu.

Kakakin ya kuma ce Kwamishinan ’yan sandan Jihar, ya gargadi bata-gari cewar basu da maboya a Jihar, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci fushin hukuma.