Home Labaru Kiwon Lafiya Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Hukumar Nafdac Ta Lalata Kwayar Tramadol Ta Naira...

Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Hukumar Nafdac Ta Lalata Kwayar Tramadol Ta Naira Tiriliyan 2

42
0

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta ce ta lalata kwayar maganin Tramadol da darajarta ta kai Naira tiriliyan biyu a cikin shekara hudu.

Shugabar Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan a Abuja a lokacin da take jawabi ga manema labarai kan bikin cikarta shekara hudu tana jagorancin hukumar.

A cewarta, hukumar ta kuma samu nasarar lalata jabun magunguna da darajarsu ta kai Naira Biliyan takwas a tsawon lokacin.

Ta ce, “Domin ci gaba da tabbatar da lafiyar al’umma, hukumar ta lalata jabu, gurbatattu, haramtattu da kuma kayayyaki na sama da Naira 8,000,260,000, a sassa daban-daban na kasar nan.

Ta kuma ce akwai kalla shari’u kimanin 20 da hukumar take fafatawa da masu ta’ammali da jabun magunguna, kuma akasarinsu an yanke musu hukuncin dauri, wasu kuma na biyan tara.