Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Gano Gawarwakin ‘Yan Bindiga Hudu A Enugu

‘Yan Sanda Sun Gano Gawarwakin ‘Yan Bindiga Hudu A Enugu

280
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Enugu, ta ce jami’an ta sun samu
nasarar tarwatsa wani gungun ‘yan bindiga da ke kokarin
kakaba dokar zaman gida a jihar.

A cikin wani sako da rundunar ta wallafa a shafin ta na Twitter, ta ce a ranar Juma’ar da ta gabata ne, jami’an ta suka gano gawarwaki hudu daga cikin ‘yan bindigar a wani daji da ke garin Awkunanaw, inda su ka gudu domin buya.

Sanarwar ta ce a ranar Alhamis da ta, jami’a ‘yan sandan sun fatattaki wasu ‘yan bindiga da su ka yi yunƙurin kwace wata mota daga hannun wani direba, inda maharan su ka gudu tare da munanan raunukan harbin bindiga a jikin su.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar CP Ahmed Ammani ya tabbatar da cewa, jami’an ‘yan sanda na jihar da sauran jami’an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai sun tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar, ta yadda mazauna yankin za su rika fita harkokin kasuwancin su a kowacce rana.

Leave a Reply