Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Ceto Ɗaliban Jami’a Biyar Da Aka Sace A Zamfara

‘Yan Sanda Sun Ceto Ɗaliban Jami’a Biyar Da Aka Sace A Zamfara

1
0

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Zamfara, ta ce ta ceto ɗalibai
biyar na Jami’ar Gusau bayan masu garkuwa da mutane sun
sace su.

Kwamashinan ‘yan Sanda na jihar Mohammed Bunu, ya ce wasu mutane ne ɗauke da makamai su ka afka gidan wani mai suna Isah Mai Burodi a yankin Sabon Gari na ƙauyen Damba.

Ya ce maharan sun kuma ƙwace kuɗi Naira dubu 200 daga gidan mutumin, sannan su ka wuce gidan ɗaliban tare da sace maza biyu da mata uku.

Kwamishinan ya kara da cewa, su na samun rahoton lamarin dakarun su suka bazama, insa su ka ceto mata biyu da su ka hada da wata Blessing Matthew da Comfort Olola.

Ya ce daga baya sun sake kai samame dajin Karazau kuma da ganinsu ‘yan bindigar su ka arce tare da barin sauran ɗaliban da su ka yi garkuwa da su.