Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Cafke Ɗan Bursunan Da Ya Gudu Daga Kurkukun Kuje

‘Yan Sanda Sun Cafke Ɗan Bursunan Da Ya Gudu Daga Kurkukun Kuje

1
0

Rundunar ‘yan Sanda ta Jihar Nasarawa, ta samu nasarar
kama daya daga cikin fursunonin da su ka tsere da gidan yarin
Kuje Salisu Buhari, tare da wani abokin shi mai suna Zubairu
Ali, bayan sun saci babur a Ƙaramar Hukumar Nasarawa a
Jihar Nassarawa.

Kakakin rundunar ‘yan Sanda ta Jihar Nasarawa Ramhan Nansel ya sanar da haka a Lafiya, inda ya ce an kama gudajjen fursunan ne tare da wani abokin sa mai suna Zubairu Ali bayan sun saci babur.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa, su biyun ke da alhakin satar kusan dukkan baburan da ake sacewa a Ƙaramar Hukumar Nasarawa da kewaye.

Ramhan Nansel, ya ce Salisu Buhari da kan sa ya shaida wa ‘yan sanda cewa, daga Kurkukun Kuje ya tsere lokacin da ‘yan ta’adda su ka kai wa kurkukun hari a cikin watan Yuli na shekara ta 2022.

Kwamishinan ‘yan Sanda na Jihar Nasarawa Maiyaƙi Mohammed-Baba, ya bada umarnin a maida binciken mai laifin zuwa Ofishin Binciken Masu Manyan Laifuffuka da ke Lafiya.