Home Labaru ‘Yan Sanda 4 Da Fararan Hula 2 Sun Mutu A Harin Da...

‘Yan Sanda 4 Da Fararan Hula 2 Sun Mutu A Harin Da Boko Haram Su Ka Kai Damboa

461
0
‘Yan Sanda 4 Da Fararan Hula 2 Sun Mutu A Harin Da Boko Haram Su Ka Kai Damboa
‘Yan Sanda 4 Da Fararan Hula 2 Sun Mutu A Harin Da Boko Haram Su Ka Kai Damboa

Mayakan kungiyar boko Haram sun kashe ‘yan sanda hudu da fararan hula biyu a wani hari da su ka kai barikin soji da ke garin Damboa a jihar Borno.

‘Yan ta’addan sun kai hari ne a wasu motoci da ke dauke da manyan bindigogi, lamarin da ya ba su damar kasahe ‘yan sanda hudu da fararan hula biyu.

Wani soja da ya bukaci a sakaya sunan sa ya ce, jami’an ‘yan sanda sun gamu da ajalin su ne sakamakon sun shiga fafatawar da ‘yan ta’addan ke yi da sojojin ne.

Wani dan kato da gora mai suna Ibrahim Liman ya tabbatar da haka bayan ya taimakawa sojoji a lokacin ar’tabun, sannan kuma wani mazaunin kauye Modu Malari cewa ya yi,  ‘yan ta’addan sun kai harin ne da wasu manyan bindigogi, amma sojoji suka ci nasarar fatattakar su bayan an yi an yi gumurzu na tsawon sa’o’I biyu.

Haka kuma, ‘yan ta’addan sun raunata mutane fiye da 50 a lokacin farmaki, yayin da wasu suka gudu zuwa gidajen da ke makwabtaka da inda lamarin ya faru.

Garin Damboa dai na kusa da dajin Sambisa, inda ‘yan ta’addan Boko Haram ke boyewa domin kai hari a wasu kauyuka da kuma barikin sojoji da ke garin.