Home Home Yan Sa-Kai Sun Kashe Mutum 6 A Zamfara

Yan Sa-Kai Sun Kashe Mutum 6 A Zamfara

295
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara, ta tabbatar da kisan mutane shida, tare da raunata wasu da dama a Kadamutsawa da ke cikin masarautar kwatarkwashi a Karamar hukumar Bungudu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar ASP Yazid Abubakar ya bayyyana haka a cikin wata sanarwa da y araba wa manema labarai a Gusau.

Ya ce shugaban ‘yan sanda na Kwatarkwashi ya jagoranci hadin gwiwar jami’an soji da ‘yan sanda zuwa kauyen domin zakulo wadanda su ka aikata laifin don hukunta su.

Rundunar ‘yan sandan, ta yi kira ga ‘yan’uwan wadanda abin ya shafa su cigaba da yin hakuri tare da ba hukumomi damar gano masu laifin.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar CP Muhammed Bunu ya tabbatar wa al’ummar jihar Zamfara cewa, dole ne a daina kashe-kashe a jihar domin gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar ganin an dawo da zaman lafiya a kowane bangare na Nijeriya.

Leave a Reply