Home Home An Samu Barkewar Annobar Cutar Sarkewar Numfashi, DIPHTHERIA A Abuja

An Samu Barkewar Annobar Cutar Sarkewar Numfashi, DIPHTHERIA A Abuja

240
0

Ma’aikatar raya birnin tarayya Abuja, ta ce an samu barkewar annobar cutar sarkewar numfashi na yara da ake kira DIPHTHERIA a wasu  yankunan birnin.

Daraktan sashin kula da lafiyar jama’a na ma’aikatar Dr. Sadik Abdulrahman ya bayyana haka, inda ya ce tuni har cutar ta hallaka wani yaro dan shekaru hudu.

Dr. Sadik ya ce an yi gwaji a kan wasu mutane takwas da ke Tungar Wakilia bangaren Dei-Dei da ke wajen birnin, inda aka samu tabbacin mutum daya ya na dauke da cutar.

Ya ce a watan Janairun wannan shekarar, gwamnatin Tarayya ta ankarar da barkewar cutar a jihohin Lagos da Kano da Ondo, lamarin da ya sa hukumar kula da cututuka masu yaduwa NCDC ta ja hankalin baki da ‘yan jihohin Nijeriya da Abuja.

Dr. Sadik Abdulrahman, ya ce alamun cutar sun hada da zazzabi da yoyon majina da kumburin kafafu da tari da kuma kankarewar wuya da haddasa mutuwa.

Leave a Reply