‘Yan Nijeriya sun yi barazanar yin bore, muddin gwamnatin tarayya ta gaza daukar matakin dakatar da bankin CBN a kan wa’adin da ya bada na daina karba da kuma amfani da tsofaffin takardun kudin da aka sauya wa fasali.
Shugaban Kungiyar Matasan Arewa maso Gabas Alhaji Abdulrahman Buba Kwacha, ya ce matakin zai takura wa talaka tare da kai shi bango kuma su ba za su yarda da lamarin ba.
‘Yan Nijeriya da dama dai sun yi korafi game da karancin sabbin takardun kudin, inda su ka ce har yanzu bai wadata ba, kuma har yanzu bankuna tsofaffin takardun kudi su ke ba mutane.
Mataimakin Shugaban Kungiyar Sauya Tattalin Arzikin Arewacin Nijeriya Abubakar Muhammad Kantato, ya ce wa’adin da bankin CBN ya bada ba karamin ruguza tattalin arzikin yanki arewa zai yi ba, la’akari da ‘yan kasuwar da ke kauyukan da babu bankuna.
Gammayyar kungiyoyin arewacin Nijeriya, ta yi kira ga ‘yan Nijeriya su fito su nema wa kan su mafita a kan wannan lamari, kamar yadda shugaban ta Nastura Ashir Shariff ya bayyana.
You must log in to post a comment.