Home Labaru Masu Kutse Daga Ketare Na Kai Hari Kan Bayananmu Na Sirri –...

Masu Kutse Daga Ketare Na Kai Hari Kan Bayananmu Na Sirri – INEC

65
0

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce ana yawan samun yunƙurin kutse ga tsarin komfutocin su lokacin da su ke fuskantar zaben shekara ta 2023.

Mahmud Yakubu ya bayyana haka ne, yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja, wanda aka yi wa take da Zaɓen 2023 tare da tabbatar da dimokradiyya mai dorewa.

Farfesa Mahmud, wanda mataimakin daraktan kula da fasahar zamani Dr Lawrence Bayode ya wakilta, ya ce hare-haren da ake fuskanta ana samun su ne daga sassa daban-daban na duniya ba Nijeriya kadai ba.

Ya ce su na cikin duba komfutocin su, sai kawai su ka ga wasu mutane daga Faransa su na neman yi masu kutse, amma nan take suka ɗauki mataki.

Leave a Reply