Home Labarai ‘Yan Majalisar Wakilai 6 Sun Koma PDP Daga APC A Jihar Zamfara

‘Yan Majalisar Wakilai 6 Sun Koma PDP Daga APC A Jihar Zamfara

340
0

‘Yan majalisar wakilai Shida da su ka koma jam’iyyar APC tare da gwamna Matawalle na jihar Zamfara, sun sake komawa jam’iyyar PDP, sun kuma karɓi tikitin takara ba tare da hamayya ba.

Wata majiya bta ce, ‘yan majalisar sun sake komawa PDP ne sakamakon yarjejeniyar da aka yi yayin sulhun gwamna Matawalle da Abdul-Aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa.

Rahotanni sun ce, jam’iyyar APC ta hana ‘yan majalisun damar sayen Fom na tsayawa takara a zaɓen shekara ta 2023 saboda ta riga da ta ba wasu sabbi kujerun su.

‘Yan majalisar dai sun ha]a da Ahmad Maipalace da Bello Hasan da kuma Sulaiman Gummi na mazaɓar Gummi da Bukkuyum.

Sauran sun ha]a da Sani Umar da Shehu Ahmad da kuma Ahmad Muhammed mai wakiltar mazaɓar Bakura da Maradun a majalisar wakilai.

Leave a Reply