Fadar shugaban kasa ta gargadi ‘yan Nijeriya a kan yunkurin maida martani, bisa bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta na kisan wata ‘yar Arewa mai juna biyu tare da ‘ya’yan ta hudu a jihar Anambra.
A cikin wata sanarwa da ya fiyar, mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya ce Shugaba Buhari ya yi kira ga ‘yan Nijeriya kada su yi gaugawar yanke hukunci a kan bidiyon.
Ya ce masana su na gudanar da bincike a kan bidiyon domin sanin ko gaskiya ne ko ba gaskiya ba ne.
Sanarwar, ta ce Fadar shugaban kasa ta na gargadi a kan yunkurin tada tarzoma da lalata dukiya ko maida martani a kan bidiyon da ake zargin ‘yan kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra da kashe yan ci rani.
Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi Allah-wadai da kashe-kashen mutanen da ake yi a yankin kudu maso gabas da wasu sassan Nijeriya.