Home Labaru ‘Yan Majalisa ‘Za Su Tabbatar Da Dokar Da Buhari Ya Ki Sanya...

‘Yan Majalisa ‘Za Su Tabbatar Da Dokar Da Buhari Ya Ki Sanya Wa Hannu’

100
0

Sama da ‘yan majalisa 73 sun bayyana aniyar amfani da karfin iko wajen tabbatar da sabuwar dokar zaben da shugaba Muhammadu Buhari ya ki sanyawa hannu.

Jaridar Premium Times ta ambato Sanata George Sekibo daga jihar Rivers na cewa tuni ‘yan majalisar daga jam’iyyu daban-daban suka fara sanya hannu kan takardar amincewar.

Mr Sekibo wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP ne, ya kara jaddada aniyarsu a tattaunawa da gidan talbijin na Channels, a ranar Talata.

An ambato Mista Sekibo na cewa: “Don me ya sa shugaban kasa zai ki amincewa da zaben fidda kwani na ‘yar tinke? Najeriya ba kamfaninsa ba ce, wannan kasa ce da cikakken iko da kuma ta ke da ‘yan majalisu. Kuma za mu tabbatar da wannan doka.

“Sashe na 58 na kundin tsarin mulki ya ba mu damar daukar matakin. Dan haka idan tsarin mulki ya ba mu dama, za mu yi amfani da hakan. Kuma tuni mu ka samu ‘yan majalisa 73 daga jam’iyyu daban-daban da suka rattaba hannun amincewa da matakin tabbatar da dokar nan, za kuma mu yi hakan.’

Leave a Reply