Mutum guda ya mutu yayin da ake ci gaba da neman wasu 70, bayan zabtarewar kasa a wurin hakar ma’adinai ta Jade da ke arewacin Myanmar.
Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutanen da akai amanna yawancinsu masu hakar ma’adinai ne ba bisa ka’ida ba.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a yankin Hpakant da ke jihar Kachin da misalin karfe 4 agogon kasar.
Kasar Myanmar ita ce sahun gaba a duniya da ta ke samar da ma’adinin Jade, sai dai ana yawan samun hatsari irin na zabtarewar kasa a wuraren hakar kasar.
Kwanakin da suka gabata, mutum 10 ne suka bata a wata zabtarewar kasar a dai wurin hakar ta ma’adinan Jade.
Hukumomin Myanmar sun haramta hakar ma’adinin Jade, amma mazauna kauyukan da ke kusa da wurin na satar jiki domin hakowa sakamakon rashin aikin yi da samun abin da za su ciyar da iyali, wanda barkewar annobar cutar korona ta kara musu tsananin wuya.
You must log in to post a comment.