Wasu karin‘yan majalisar dokoki ta jihar Kano uku sun sauya she]a daga jami’iyyar APC zuwa jam’iyyar NNPP.
Kakakin majalisar Uba Abdullahi ya sanar da haka, inda ya ce ‘yan majalisar sun sanar da sauya shekar ne a wasi}un da su ka aike wa kakakin majalisar.
‘Yan majalisan da su ka sauya shekar dai sun ha]a da Abdullahi Iliyasu Yaryasa Mai wakiltar Tudun Wada, da Muhammad Bello Butu-Butu Mai wakiltar Tofa da Rimin Gado da kuma Kabiru Yusuf Isma’ila na Madobi.
Haka kuma, ‘yan majalisar sun ce sun yi haka ne saboda matsalolin shugabanci da Jam’iyyar ke fama da su.














































