Home Home Yajin Aiki: Dalibai Sun Rufe Hanyoyin Ife-Ibadan Da Lagos-Abeokuta

Yajin Aiki: Dalibai Sun Rufe Hanyoyin Ife-Ibadan Da Lagos-Abeokuta

21
0

Wasu daliban jami’a sun yi zanga-zanga don ganin an kawo }arshen yajin aikin }ungiyar ASUU, sannan su ka ce za su cigaba da yin bore har sai malaman jami’o’i sun janye yajin aikin da su ke yi tare da sake bu]e makarantu don ci-gaba da karatu.

Daruruwan daliban ne su ka rufe manyan hanyoyin da su ka tashi daga Ibadan da Elesa da ke kusa da jami’ar Oduduwa.

Wani bidiyo ya nuna ]aliban su na cewa ba su jin tsoron jami’an tsaro, tare da barazanar zaman dirshan a kan tituna har sai an bu]e jami’o’in.

Daliban sun bayyana takaicin su a kan yadda ake ci-gaba da yajin aikin, sun kuma nuna takaici a kan ‘yan siyasa dangane da yadda su ka kauda kai daga ba}atun su, inda ba su taka rawar da ta dace wajen tabbatar da an biya wa malaman jami’o’in bu}atun su.

Maimakon haka, sun maida hankali a kan sayen Fom domin tsayawa takara a shekara mai zuwa.