Home Home ‘Yan Daba Ɗauke Da Makamai Sun Kai Hari Wurin Gangamin Taron Atiku...

‘Yan Daba Ɗauke Da Makamai Sun Kai Hari Wurin Gangamin Taron Atiku A Kaduna

566
0
Wasu ‘yan daba sun kai wa magoya bayan jam’iyyar PDP a wajen taron gangamin ɗan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar hari a Kaduna.

Wasu ‘yan daba sun kai wa magoya bayan jam’iyyar PDP a wajen taron gangamin ɗan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar hari a Kaduna.

Atiku Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook, infda ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya umarci sauran jam’iyyu su dakatar da magoya bayan su daga yunkurin tada yamutsi a wurin taro.

Ya ce ya samu labarin cewa wasu ‘yan daba da aka ɗauki nauyin su sun kai wa magoya bayan PDP hari, da zummar tada hargitsi da tarwatsa taron gangamin jam’iyyar PDP a jihar Kaduna.

Atiku Abubakar, ya ce harin ya saɓa wa Demokaraɗiyya, kuma ya saɓa wa yarjejeniyar zaman lafiya da jam’iyyu su ka sanya wa hannu makonni kadan da su ka gabata.

A karshe ya roki shugaba Muhammadu Buhari ya kira jam’iyyu su gaggauta dawo da magoya bayan su cikin hayyacin su, domin tabbatar da an yi gangamin yakin neman zabe da zaɓen kan sa cikin kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY