Home Home Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin shi ta duƙufa a kan...

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin shi ta duƙufa a kan ƙoƙarin magance tsadar farashin abinci a Nijeriya.

512
0

Buhari ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke buɗe taron bita a kan ayyukan ministocin sa karo na uku domin tantance irin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da ƙudurorin da gwamnatin sa ke ba fifiko.

Ya ce su na gagarumin ƙoƙari domin warware matsalar tashin farashin abinci mai alaƙa da hauhawar farashin da ake fama da shi a faɗin duniya.

Shugaba Buhari, ya ce alƙaluman baya-bayan nan daga Hukumar Ƙididdiga ta kasa sun nuna cewa, hauhawar farashi a Nijeriya ta kai sama da kashi 20 a watan Satumba.

 Buhari ya ce gwamnatin shi ta aiwatar da ayyukan raya ƙasa masu gagarumin tasiri, don haka shugabancin shi ya cimma muradai da bukatun ‘yan Nijeriya.

Leave a Reply