Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Zama Jiha Mai Zaman Kan Ta A Jihohin Arewa...

‘Yan Bindiga Sun Zama Jiha Mai Zaman Kan Ta A Jihohin Arewa Maso Yamma – Shehu Sani

33
0

Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya ce ‘yan bindiga sun zama jiha mai zaman kan ta a yankin arewa maso yammacin Nijeriya.

Shehu Sani, ya koka ne yayin wata hira a gidan talbijin na Channels, inda ya ce ‘yan bindiga a Arewa maso yamma sun zama jiha mai zaman kan ta a cikin jiha, domin sun yi nasarar kafa tsarin gwamnati, ta yadda har ta kai su na su na nade-nade sarauta

‘Yan bindiga dai na ci-gaba da kai munanan hare-hare a jihohin Kaduna da Zamfara da Sokoto da Katsina da Neja, inda su ke kashewa tare da yin garkuwa da mutane.

Sanatan ya kara da cewa, ya kamata gwamnati ta kara kaimi wajen tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, domin wurare da dama a yau su na karkashin ikon ‘yan bindiga.