Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 10 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 10 A Zamfara

243
0
Gunmen kill health worker abduct two wives four children in Jangebe
Gunmen kill health worker abduct two wives four children in Jangebe

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Moriki da ke jihar Zamfara a daren Laraba, inda suka yi garkuwa da mutane sama da.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin,

inda ya kuma bayar da tabbacin cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarci jami’an rundunar su kai dauki domin ceto wadanda lamarin ya shafa.

Wani mazaunin garin na Moriki ya shaida wa manema labarai  cewa ‘yan bindigar sun fitini al’umma, kuma bayan tun da farko sun yi garkuwa da wasu mutanen yankin.

Sannan ‘Yan bindigar sun bayyana cewa sun kai harin ne bayan Kwamandan ƴan sakai ya kashe shanun su,

a yayin da suka bi gida-gida suna zabar mutane, sannan kuma suka yanke za a biya su Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa.

Leave a Reply