Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matafiya Da Dama A Jihar Ondo

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matafiya Da Dama A Jihar Ondo

311
0

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da dama a kan babbar hanyar Benin zuwa Owo a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo.

Wata majiya ta ce, matafiyan su na cikin wata babbar mota kirar Bas ne daga jihar Benin zuwa jihar Ondo.

Yayin da ta ke tabbatar da lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo Funmilayo Odunlami, ta ce ba za ta iya tabbatar da adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.

Sai dai ta ce tuni jami’an tsaro sun fara bincike domin gano tare da kubutar da mutanen da aka sace.

Leave a Reply