Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC a jihar Adamawa, ya tsige shugaban jam’iyyar Ibrahim Bilal daga kujerar sa bisa zargin cin amana da sama da faɗi da kuɗaɗe da karya dokokin jam’iyya.
Tuni dai an rantsar da mataimakin sa Ismaila Tadawus a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar Adamawa tare da amincewar Ofisoshi 24 daga cikin 36.
A wani taro da ya gudanar a Sakatariyar jam’iyya da ke Yola, Kwamitin ya zargi tsohon shugaban da amfani ƙarfin iko wajen kwashe kuɗaɗe.
Kakakin jam’iyyar APC na jihar Muhammed Abdullahi, ya ce sun zargi Bilal ne da yin watsi da Sakatariya tsawon watanni biyu, kuma bai halarci taron zaben fidda ɗan takarar gwamna ba.
Abdullahi ya kara da cewa Bilal, ya gaza kare kan sa a kan tuhume-tuhumen da ake yi masa, sannan ya yi watsi da hakkin da ya rataya a wuyan sa ya gudu zuwa Abuja, a daidai lokacin da jam’iyya ke bukatar sulhunta fusatattun ‘ya’yan ta.
Ya ce shugaban jam’iyyar ya yi amfani da shafin sa na Facebook, wajen rokon mutane su kaurace wa ‘yar takarar gwamna ta jam’iyyar APC su zaɓi Sanata Ishiaku Abbo na jam’iyyar NNPP.














































