‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani ma’aikacin hukumar
birnin tarayya Abuja tare da wasu akalla mutane 15 a rukunin
gidaje da ke Pegi a karamar hukumar Kuje.
Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Lahadin da ta gabata, inda su ka yi ta harbe-harbe, sannan su ka yi awon gaba da mutanen da su ke komawa gida daga aiki.
Shugaban kungiyar mazauna garin Pegi Taiwo Aderibigbe ya bayyana wa manema labarai haka a Abuja, inda ya ce daga cikin wadanda aka sace akwai ma’aikatan sashen kula da ci- gaban birnin tarayya Abuja.
Aderibigbe, ya ce ‘yan bindigar sun sace mutane 15 a kan titin Pegi, kuma daga cikin su akwai ma’aikacin hukumar birnin tarayya Abuja Shu’aibu Musa,.
Ya ce masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi iyalan wadanda su ka sace ba a halin yanzu, amma har yanzu su na kokarin gano wasu mazauna garin da aka sace.
You must log in to post a comment.