Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa, ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Rijiya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane shida.
Wani mazaunin garin, ya ce da tsakar rana maharan su ka afka wa kauyen a kan babura da harbe-harbe, inda har su ka sace matan da har yanzu ba a iya tantance adadin su ba.
Ya ce akwai mutanen da ke kwance asibiti da suka ji rauni a harin, kuma daga cikin waɗanda maharan suka tafi da su har da yara ƙanana.
Jihar Zamfara dai ta na fama da hare-haren ‘yan bindiga, duk kuwa da matakan da hukumomi su ka ɗauka ciki har da rufe layukan sadarwa da dakatar cin kasuwannin mako-mako da sauran su.
Mutanen yankin sun shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindiga sun addabe su saboda rashin jami’an tsaro.
You must log in to post a comment.