Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗanmudi Na Mada Dalilin Kashe Gogarman

‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗanmudi Na Mada Dalilin Kashe Gogarman

39
0

Mazauna garin Mada da ke karamar hukumar Gusau a jihar Zamafara, su na ci-gaba da yin ƙaura daga garin saboda fargabar ‘yan bindiga za su iya kai masu hari a kowane lokaci.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ta tabbatar da haka, ta na
mai cewa tuni ta aika jami’an ta su kai wa mutane ɗauki, tare da
tabbatar da zaman lafiya a garin Mada.

Wani mazaunin garin Mada mai suna Yusuf Anka ya shaida wa
manema labarai cewa, harin ramuwar gayya ne ya kai ‘yan
bindiga garin na Mada.

Ya ce kwanakin baya ‘yan banga sun kai wa ‘yan bindiga hari,
inda su ka hallaka wani jagoran su mai suna Mala’ikan
Hausawa, wanda burin sa a kullum shi ne ya ga bayan duk wani
Bahaushe da ya yi gaba da gaba da shi.

Yusuf Anka, ya ce jagoran ‘yan banga ya kai farmaki
sansanonin ‘yan bindigar, inda ya kashe mahara da dama ciki
har da Mala’ikan Hausawa, shi ya sa ‘yan bindigar su ka yi
shirin musamman su ka afka garin Mada.