Home Labarai ‘Yan Ta’adda Na Shirin Kai Hari Masallatai Da Wuraren Shaƙatawa – DSS

‘Yan Ta’adda Na Shirin Kai Hari Masallatai Da Wuraren Shaƙatawa – DSS

223
0

Hukumar jami’an tsaro na farin kaya SSS, ta ce ta gano wani shiri da wasu bataigari ke yi na kai hare-hare a muhimman gine- gine, da wuraren ibada da wuraren shakatawa musamman yayin bukukuwan Karamar Sallar da bayan sallah.

A cikin wata sanarwa Kakakin hukumar Peter Afunanya ya fitar,
ya ce bata-garin su na neman maida Nijeriya tamkar kafin
shekara ta 2015, lokacin da aka rika sanya boma-bomai a wasu
sassan kasar nan.

Ya ce hukumar ta gano shirin da wasu bata-gari ke yi na hadin
gwiwa, domin kai hare-hare a kan wasu muhimman gine-gine da
wuraren da mutane ke taruwa kamar wurin ibada da wuraren
shakatawa musamman lokacin bikin sallah da bayan sallah.

Hukumar SSS, ta ce ba za ta yi kasa gwiwa ba wajen ganin ta
samar da tsaro ta hanyar hadin gwiwa da sauran hukumomin
tsaro, domin tabbatar da cewa mutane sun cigaba da rayuwa
cikin lumana.

Leave a Reply