Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Ɗana Bom A Ofishin Yan Sanda, Sun Halaka Babban Jami’i...

‘Yan Bindiga Sun Ɗana Bom A Ofishin Yan Sanda, Sun Halaka Babban Jami’i A Kogi

42
0

‘Yan bindiga sun kai hari Ofishin ‘yan sanda na yankin Eika- Ohizenyi da ke ƙaramar hukumar Okehi ta jihar Kogi.

Bayanai sun nuna cewa, ‘yan bindiga sun kai harin ne ɗauke da Boma-Bomai da sanyin safiyar Jumu’a, inda wani Jami’in ɗan sanda mai muƙamin sufeta ya rasa ran sa, yayin da aka yi kaca- kaca da wani jami’in dan sanda.

Wani mazaunin yankin Mallam Momoh Abubakar, ya ce maharan sun mamaye ofishin ‘yan sandan ne ɗauke da Boma- bomai da wasu makamai.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kogi William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya ce tuni Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edward Egbuka ya ziyarci wurin da lamarin ya faru.

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya ba da umarnin a ƙara girke jami’an tsaro a yankin domin maido da zaman lafiya a kuma kwantar wa mutane hankali.