Home Labarai Yadda Ta Kasance Tsakanin Shugaba Buhari Da Firayin Minstan Birtaniya A Taron Chogm

Yadda Ta Kasance Tsakanin Shugaba Buhari Da Firayin Minstan Birtaniya A Taron Chogm

24
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jaddada wa Firayin ministan Birtaniya Boris Johnson aniyar sa ta sauka daga mulki a shekara ta 2023.

Buhari ya shaida wa Boris Johnson haka ne a yayin wata ganawar diflomasiyya da su ka yi a wajen taron ƙasashe renon Ingila a ƙasar Rwanda.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, ta ce Boris Johnson ne ya tambayi Buhari ko zai sake tsayawa takara, wataƙila kasancewar bai san yadda tsarin Nijeriyar ya ke ba.

Sai dai Shugaba Buhari ya amsa da cewa ba zai yi ta-zarce ba, domin ko wanda ya taba yii ƙoƙarin zarcewa bai ƙare lafiya ba.