Home Labaru ‘Yan Bindiga Na Ƙona Amfanin Gona Idan Ba A Ba Su Kuɗi...

‘Yan Bindiga Na Ƙona Amfanin Gona Idan Ba A Ba Su Kuɗi Ba A Jihar Zamfara

100
0

Manoma a wasu yankunan jihar Zamfara, sun ce ‘yan bindiga sun fara ƙona amfanin gonar su.

Al’ummar yankin Magami da ke ƙaramar hukumar Gusau, sun ce lamarin ya na ƙara jefa su cikin mummnan yanayi, su na masu cewa hakan zai iya janyo matsalar ƙarancin abinci.

Wani mazauni yankin da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce ‘yan bindiga sun sanya wa ƙauyukan yankin haraji, kuma matuƙar ba a biya ba su kan matsa masu da sace duk mutanen da su ka yi kasadar zuwa gona ko kuma su ƙone amfanin gonar sa. 

Ya ce yanzu haka ‘yan bindigar gonaki biyu su ka cinna ma wuta a Magami ranar Litinin da ta gabata, sai dai rundunar ‘yan sanda ta jihar ta musanta bayanan ƙona amfanin gonar, inda ta ce ba a kai mata wani rahoto game da lamarin ba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara SP Muhammad Shehu, ya ce a hukumance ba su samu rahoton ba, amma idan har akwai waɗanda su ka yi ƙorafin sai su sanar da jami’an tsaro.