An kashe mutum daya, sannan ba a ga wasu da dama ba bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Isin ta Jihar Kwara.
Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun tare hanyar Ijara zuwa Isin ne, inda suka sace matafiya da dama tare da kashe wani mai suna Cif Adeyemi a yankin Pamo Isin.
A wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizo, an gargadi mazauna yankin game da bin hanyar, saboda an sace wasu matafiya da ba a san adadin su ba.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kwara SP Okasanmi Ajayi ya tabbatar da faruwar lamarin a birnin Ilorin.