‘Yan sanda a jihar Neja sun ceto mutum 20 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su sakamakon samamen da suka kai kan sansanin ‘yan fashin daji a jihar da ke tsakiyar Najeriya.
Kakakin rundunar a Neja, DSP Wasiu A. Abiodun, ya faɗa cikin wata sanarwa a ranar Lahadi cewa dakarun su sun kai samamen ne a yankin Anaba da ke Ƙaramar Hukumar Magama.
Bayan fafatawa gami da harbe-harbe tare da ‘yan bindigar, dakaru sun yi nasarar kashe ‘yan fashin tare da ƙwato shanun da suka sata.
Ya ce Ƙarin dakarun da aka tura ciki har da sojoji da ‘yan banga sun fara fafatawa da ‘yan bindigar a kan hanyar shanu da Ibeto kusan tsawon awa biyu a lokacin da maharan ke ƙoƙarin guduwa.
A cewar DSP Abiodun, daga cikin makaman da aka ƙwace daga hannun su sun haɗa da bindigar AK-47 ɗaya da ƙunshin harsasai 30 da wayar salula bakwai da babur ɗaya.














































