Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Bindiga Fiye Da 50...

Yaki Da Ta’addanci: Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Bindiga Fiye Da 50 A Jihar Kaduna

26
0

Rahotanni daga Najeriya sun nuna cewa rundunar sojin sama na samun nasara a hare-hare ta sama da take kai wa sansanonin ‘yan fashin daji da ke jihar Zamfara da kuma Kaduna.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa jiragen Rundunar sojojin sama sun kai hari a sansonin yan fashin dajin da ke dajin Kawara a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.

Wata majiyar tsaro ta ce ‘yan fashin daji kusan hamsi ne suka hallaka a hare-haren ta sama a karshen mako

Majiyar ta kuma ce wani jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojin sama ya gano wani gungun yan fashin daji sanye da bakaken tufafi, tare da shanu da suka sace kusa da kauyen Kawara a karamar hukumar Giwa.

Jiragen saman dai sun yi luguden wuta a sansanonin ‘yan fashin daji a Zamfara