Home Labarai Yaki Da Ta’Addanci: Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’Adda 80 a Arewa Ta...

Yaki Da Ta’Addanci: Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’Adda 80 a Arewa Ta Tsakiya – DHQ

95
0

Helkwatar tsaro da ke Abuja, ta bayyana yadda dakarun soji su
ka samu nasarar hallaka ‘yan ta’addan akalla 80 cikin makonni
biyu a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Daraktan yada labarai na sojin Manjo Janar Bernard Onyeuko ya
bayyana haka, yayin tattaunawa da manema labarai dangane da
ayyukan da sojojin su ka aiwatar tsakanin ranar 25 ga watan
Maris zuwa 7 ga watan Afirilu a Abuja.

Manjo Janar Onyeuko, ya ce a Jihohin Kaduna da Neja,
rundunar Operation Thunder Strike ta samu nasarar kashe ‘yan
ta’adda 34, tare da kwace bindigogin toka guda 14 da babura 17
daga hannun su.

Ya ce a ranar 30 ga watan Maris, rundunar sojin sama ta aiwatar
da harbe-harbe ta sama a kan ‘yan ta’addan da ke kan Babura a
titin Akilbu zuwa Sarkin Pawa da ke kauyen Mangoro tsakanin
Jihar Kaduna da Neja kuma sun halaka wasun su da dama.