Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Rundunar Sojin Sama Ta Najeriya Ta Kammala Gyaran Jiragen...

Yaki Da Ta’addanci: Rundunar Sojin Sama Ta Najeriya Ta Kammala Gyaran Jiragen Yaki 3 – Saddique

564
0

An kammala gyara  jiragen yaki dake makarantar koyan tukin jirgi a jihar Kano, kuma za’a mayar da su filin daga domin ci gaba da yaki da ‘yan bindiga a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

An gyara jiragen ne bayan shekaru ba’a amfani da su, sai da aka gayyato injiniyoyi daga kamfanin jiragen Vodochody, daya daga cikin manyan kamfanonin jiragen yaki daga kasar Czech.

An gudanar da gyaran ne tare da wasu injiniyoyin hukumar sojin saman Najeriya, inda aka kwashe watanni hudu ana aiki domin kara musu ilimi saboda iya aikin da kansu.

A wani biki da aka shirya na musamman, jakadan kasar jamhuriyyar Czech a Najeriya, Marek Sakoli, ya mikawa babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Mashal Abubakar Saddique, lambar yabo tare da tabbatar da cewar Najeriya za ta yi nasara.

A jawabin sa, Saddique Abubakar, ya ce an yanke shawarar gyaran wadanda jirage ne, domin tayar da jiragen da kasa don a yi amfani da su yau da kullum. Saddique Abubakar,  ya bayyana hadin gwiwar a matsayin wani salo na yaki da ta’addanci domin ilmantar da jami’an sojin Najeriya.