Tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP Olisa Metuh, ya bayyana cewa ya karbi kudi Naira miliyan 400 daga hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba hannun Sambo Dasuki ba.
Hukumar yaki da cin hancin da rashawa na tuhumar Metuh da laifin karbar kudi Naira miliyan 400 da kamfanin sa mai suna Destra Investment Limited.
Metuh, ya bayyana hakan ne a lokacin da ake ci gaba da sauraren karar da aka shigar kansa, inda ya bada labarin ganawarsu da Jonathan, inda ya bashi kudi Naira miliyan 400 dan ya gudanar da aikin kasa.
Ya bayyana kyawawan halin Dasuki, wanda ya ce wannan kyawawan halayen ne yasa Dasuki ya yi suna a aikinshi na soja kuma ya yi wa kasa hidima ta fannoni daban-daban.
Ya ce zuwa ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 2015, babu wani mahaluki ko kungiyar da ya taba sa kokwanto game da amanar Dasuki, balle a yi tunanin kama shi ko kai shi kara kotu a bisa zargin ya yi wani laifi.Mai shari’a Okon Abang, ya dage shari’ar sai ranar 24 ga watan Yuni 2019 domin ci gaba da sauraren karar.