Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Mun Kama ‘Yan Boko Haram 5,475 – Buratai

Yaki Da Ta’addanci: Mun Kama ‘Yan Boko Haram 5,475 – Buratai

421
0
Janar Tukur Buratai, Shugaban Dakarun Sojin Nijeriya
Janar Tukur Buratai, Shugaban Dakarun Sojin Nijeriya

Shugaban rundunar sojin kasa ta Nijeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce jami’an soji sun kama mayakan kungiyar boko hamar 5,475 tare da hallaka wasu dubbai.

Buratai ya bayyana hakan ne a taron karrama hukumomin tsaro da ya gudana a birnin Dubai hadaddiyar daular larabawa.

Buratai wanda ya samun wakilcin shugaban shirye-shiryen hukumar, Laftanan Janar Lamidi Adeosun, ya ce hukumar ta ragargaza masana’atun hada bama-bamai 32 na mayakan Boko haram, sannan an  nakasa yan ta’addan da dama, sakamakon yadda yawan su ya ragu daga dubu 35 zuwa kasa da dubu 5.

Haka kuma, ya ce hukumar Sojojin ta rasa Sojoji da hafsoshin ta a lokacin wannan yaki, sai dai duk da haka ya yaba da kokarin Sojin Nijeriya wajen samun nasara a kan ‘yan Boko Haram.

Buratai ya ce, kididdiga daga hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta nuna cewa, mayakan Boko Haram sun kashe mutane dubu 30 zuwa dubu 100, sannan mutane miliyan biyu sun bar muhallin su, wanda yanzu haka su ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijra 35.