Cibiyar yaki da rashawa ta kungiyar kasashen Afirka, ta karrama shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu a matsayin gwarzon yaki da rashawa a nahiyar Afirka baki daya.
Kungiyar ta sanar da karrama Magu da lambar yabo ta ‘Jagoran yaki da rashawa na musaman a Afirka’ ne a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Wakilin Nijeriya a majalisar Dakta Tunji John Asaolu ya bayyana haka, inda ya ce za a karrama Magu ne saboda kwazo, da kwarewa da kuma kokarin da ya ke nunawa wajen yaki da rasahwa a Nijeriya.
Ya ce su na sa ran karramawar za ta karfafa yaki da rashawar da shugaba Muhammadu Buhari ke yi a Nijeriya.
Mista Tunji ya ce, za a gudanar da bikin karramawar ne a dakin taro na Ladi Kwai da ke Otal din Sheraton a birnin tarayya Abuja, da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba na shekara ta 2019.