Home Labaru Yaki Da Rashawa: EFCC Za Ta Daukaka Kara A Kan Waripamo Owei-Dudafa...

Yaki Da Rashawa: EFCC Za Ta Daukaka Kara A Kan Waripamo Owei-Dudafa Da Kotu Ta Saki

262
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, za ta daukaka kara a kan hukuncin da wata babbar kotu da ke Lagos ta yanke,inda ta bada belin tsohon hadimin Jonathan Waripamo Owei-Dudafa da wani ma’aikacin Banki Iwejuo Joseph..

Waripamo Owei-Dudafa

EFCC dai ta tsara daftarin daukaka karar ne bisa amfani da sashe na 241 (1) na kundin tsarin dokokin Nijeriya na shekara ta 1999.

A cikin korafin hukumar, EFCC ta ce tun a karon farko alkalin kotun yayi kuskure na sakin wadannan ake tuhuma, duk da cewa akwai laifuffuka da dama da ake zarginsu da aikatawa.

A cikin daftarin korafin da jami’in hukumar EFCC Rotimi Oyedepo ya rubuta, akwai maganar cewa alkalin ya sabawa wata dokar shari’a da ake aiki da ita wajen yanke irin wannan hukunci.

Dudafa da Iwejuo dai sun bayyana wa kotun cewa ba su san juna ba,amma hukumar EFCC ta ce wannan ba wani abu ne da zai sa a sake su ba, kasancewar hakan hali ne na ‘yan damfara, inda a karshe ta roki kotu ta sake bada izinin tsare mutanen biyu bisa la’akari da kundin tsarin dokokin hukumar EFCC na shekara 2004, da kuma dokar da ta haramta almundahanar kudade ta shekara ta 2011.