Home Labaru Kimanin ‘Yan Gudun Hijira 25,000 Sun Koma Gidajen Su A Jihar Zamfara...

Kimanin ‘Yan Gudun Hijira 25,000 Sun Koma Gidajen Su A Jihar Zamfara – Hukuma

735
0

Kimanin ‘yan gudun hijira dubu 25ne suka koma gidajensu dake kauyukan jihar Zamfara, biyo bayan fadi-tashin da Gwamnan Bello Matawalle ya yi domin samar da zaman lafiya a jihar.

Shugaban hukumar bada agajin gaugawa na jihar Zamfara Sanusi Kwatarkwashi ya bayyana wa manema labarai haka a Gusau.

Kwatarkwashi ya ce jihar Zamfara ta samu adadin ‘yan gudun hijara dubu 37a lokacin da hare-haren ‘yan bindiga suka yi kamari.

Ya ce wadanda suka koma gidajen nasu, sun cigaba da sana’o’in da suka saba yi, inda wasu ke noma yayin da wasu ke gudanar da harkokin kasuwanci.

Kwatarkwashi ya kara da cewa, sauran mutane dubu 12 sun bazu ne a jihohin Katsina da Kaduna da Kebbi da Sokoto da kuma wani sashe na Jamhuriyar Nijar.

Ya kuma bada tabbacin cewa, gwamnatin jihar Zamfara a shirye take domin maido da sauran ‘yan gudun hijirar gida matukar zaman lafiya ya samu a garuruwansu.