Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi farin ciki kan samun nasarorin gwamnatinsa wajen dawo da dukiyar kasa.
Malami, ya bayyana hakan ne a yayin bikin bayar da kyaututtuka na shekarar bara da aka gudanar a ma’aikatar shari’a ta kasa dake Abuja.
Abubakar Malami wanda ya sami wakilcin mai Magana da yawunsa Salihu Othman Isah, ya ce ma’aikatar shari’a ta taka mataki na samun nasarori musamman a bangaren yaki da rashawa tare da wasu muhimman ababe na matse lalitar gwamnati gami da kwazon ta wajen rage cunkoso a gidajen yari. Ministan, ya bayyana yadda ma’aikatar sa ta yi kwazo wajen dawo da dukiyar kasa da gwamnatocin baya suka sace, tare da jajircewa wajen shimfida ingantattun tsare-tsare.
You must log in to post a comment.