Home Labaru Yaki Da Rashawa: An Sauya Alkalin Da Ke Binciken Ayodele Fayose A...

Yaki Da Rashawa: An Sauya Alkalin Da Ke Binciken Ayodele Fayose A Kotu

425
0

Wata babbar kotun tarayya da ke Legas, ta tsaida ranar da za a cigaba da shari’a tsakanin hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC da tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose.

Kamar yadda rahotanni sun ce kotun za ta cigaba da zama ne a ranar Juma’a 28 ga Watan Yuni na shekara ta 2019 kamar yadda Alkalin ya bayyana.

Mai shari’a Mojisola Olatotegun ce ta fara binciken karar da EFCC ta gabatar a kan Fayose da wani kamfani mai suna Spotless Investment Ltd.

Daga baya an dauke shari’ar daga hannun mai shari’a Olatoregun zuwa ga wani Alkali Chukwujekwu Aneke, biyo bayan kukan da hukumar EFCC ta kai gaban babban Alkalin kotun Abdu Kafarati.

EFCC dai ta na zargin Fayose da wasu laifuffuka 11, daga ciki akwai zargin karbar makudan kudi da yawan su ya kai Dala miliyan 5 daga hannun tsohon Minista Musiliu Obanikoro ba tare da bin ka’ida ba.